Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Dalilan da ya sanya aka rushe majalisar Masarautar Karaye

Published

on

A jiya ne sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar ya sanar da cewa ya rushe majalisar masarautar sa saboda wasu dalilai.

Sarkin ya jaddada aniyarsa ta fadada mukaman a cikin kananan hukumomi takwas 8 na Masarautar, tare da alkawarta cewa wasu daga masu rike da mukaman za su dawo yayin da wasu kuma za a daga likkafarsu zuwa gaba.

Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar na biyu ya rushe majalisarsa bayan kammala wata ganawa da duk masu rike da mukamai a Masarautar.

Babban dan majalisar Sarkin Magajin Garin Karaye Injiniya Shehu Ahmad ne ya sanar da hakan, sai dai ya ce rushewar ba ta shafi wasu Hakimai guda takwas na Masarautar ba.

Maimartaba Sarkin Karaye (Dr.) Ibrahim Abubakar ||

Wannan na kunshe ne cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na karamar hukumar Karaye Haruna Gunduwawa ya fitar a jiya.

Ya kuma jinjinawa ‘yan majalisar ta sa bisa irin gudunmawar da suka bayar wajen ciyar da Masarautar ta Karaye gaba.

Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa

Majalisar dokokin Kano zata kirkiro sababbin sarakunan gargajiya

Sarkin Karaye ya rushe majalisar masarautar sa

UNICEF:ya fara shiri na mussama ga masu rike da masarautun gargajiya

 Tarihin Masarautar Karaye:

Masarautar Karaye tana yamma da birnin Kano, yanki ne mai dausayi mai albarka da ake noma kowane nau’in abinci.

Mazaunanta na farko Maguzawa ne da habe masu sana’ar noma da farauta.

Daga baya Fulani masu sana’ar kiwo da noma suka shigo kafin Jihadin Shehu Usman Dan Fodiyo.

Yawancin Fulani sukan zo domin samun abincin dabbobinsu a bakin kogi wanda ya ratsa kasar, har suka yi kaka-gida a kasar lokaci mai tsawo, su ne suke rike da sarautar Wambai kafin Jihadi.

Da yake tattaunawa da manema labarai a kwanakin baya, daya daga cikin ’ya’yan Sarkin Karaye Alhaji Umaru Yusufu Karaye wanda masanin tarihi ne kuma marubucin littafi tarihin Masarautar Karaye mai suna “Karaye Makarar Maganar Kano.”

Alhaji Umaru Karaye, ya ce a da can Karaye akan tura Jakada domin ya rike kasa, Madakin Wambai shi ne yake rike da kasar Karaye, sai lokacin Galadiman Kano Malam Ibrahim Dabo bayan rasuwar Jakada a 1809 Malam Dabo ya dauko Baffansa a wani gari da ake kira ‘Kwazazzabon ’Yarkwando’ da ake kira Malam Kwasanlo ya sa Sarkin kano Sulaimanu ya nada shi Sarkin Kayaraye wato Hakimin Karaye.

“Kwasan ana nufin nono da Fulatanci, Kwasanlo kuma yana nufin mai kogin nono da azancin Fulatanci saboda yawan shanunsa,” inji shi.

 Asalin mazauna Karaye:

Game da asalin mazauna Karaye Alhaji Umaru Yusuf ya ce, kafin zuwan Bagauda a shekarar 999 Miladiyya, mazauna Karaye Maguzawa ne masu bautar itatuwan rimaye da kukoki.

Sunayen wadannan rimaye sune; Rimin Ya-ki-Ya-ki da Rimin Kwatan Kwano da Rimin Tagwaye da Rimin Kofar Zango.

Wadannan Maguzawa suna da shugabansu wanda ake kira Karaye, Shi ne mai lura da duk harkokin zamantakewarsu.

Maimartaba Sarkin Karaye a fadar sa.

Asalin kafuwar Karaye:

Kan asalin garin kuwa cewa ya yi: “An kafa garin Karaye a shekarar 1085 Miladiyya, kuma garin ya samo sunansa ne daga wasu manyan itatuwan da ke wata maciya wadda take tsakiyar garin.

A shekarar 1101 Miladiyya aka nada Wambai Muradu ya zama mai kula da harkokin mulkin kasar Karaye. Daga 1101 zuwa 1793 sarakunan Habe ne suke sarautar kasar karaye.”

Hakiman kasar Karaye:

Alhaji Umaru ya ce kamar yadda Kano take da tsarin nada hakimai haka Karaye take da nata tsarin nada hakiman, don haka a halin yanzu Karaye tana da hakimai kamar haka koda yake kwanan baya ta yi nadin wasu sarautu: Waziri da Madaki da Makama da Galadiman da Wambai da Chiroma da Turaki da Tafida da Damburan da Barde da Dan’isa.

Sauran su ne Yarima da Zanna da Ajiya da Dallatu da Santali da Jarma da Garkuwa da Ma’aji da Sarkin Yaki da Marafa da Talba da sauransu.

 

 

 

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!