Connect with us

Labarai

Gwamnatin tarayya bata gudanar da ayyukan tituna yadda ya kamata ba

Published

on

Ministan kudi,kasafi da stare-tsare

Ministar kudi, kasafin da tsare-tsare ta kasa, Hajiya Zainab Ahmed, ta ce  har yanzu  gwamnatin tarayya ba ta yi isasshen aikin kan ayyukan titin ba.

Ta bayyana hakan ne jiya yayin da take zantawa da manema labarai jim kadan bayan  kammala taron majalisar zartarwa ta tarayya karkashin jagorancin Mataimakin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo.

Ministan ta ce kasar nan na da titinu da dama wandada basu cikin yanayi mai kyau, suke kuma bukatar gwamnatin tarayya ta shigo ciki domin gyara su.

Ta ce daga cikin manyan tituna da ke karkashin gwamnatin tarayya mafi yawansu basu da kyau, sannan akwai sauran tituna da ke karkashin kulawa gwamnatocin jihohi da su ma ke bukatar a gyara su.

Ta kara da cewar babban abin tambaya shine,  shin gwamnati tayi aikin tituna yadda ya kamata ? sai ta ce bata yi,  hakan ne ma ya sa akwai bukatar gudanar da ayyukan tituna da samar da wani shiri na musammam da za’a tara kudade domin gyara titunan kasar na.

Ministan ta ce a shekaru biyu da suka wuce gwamnati ta bada rancen da ta kira sukuku , a shekara ta 2017 don gina tituna 25, a shekarar ta 2018 kuwa aka gina tituna 23 sannan ake aikin wasu a yanzu haka.

Da take amsa tambayoyi dangane da batun da ministan ayyukan da gidaje Babatunde Fashola yayi na cewar ma’aikatarsa bata samu kudaden da ya kamata wajen gyara tituna, sai ta ce gwamnatin tarayya bata aiwatar da ayyukan kasafin kudi kaso dari bisa dari.

Ta ce ma’aikatar ayyuka da gidaje da ma’aikatar sufiri na daga cikin ma’aikataun da suke samun kulawar da ta dace daga gwamnatin tarayya a duk lokacin da aka fitar da kasafin kudi ko wasu kudade na yin mayan ayyuka.

Ta ce ma’aikatar ta na shirin fitar da naira biliyan 900 domin gudanar da ayyukan a watan disamban nan mai zuwa.

Ta ce tuni dai shugaba Buhari ya bada umarnin  fitar da biliyan 650 domin gudanar da manyan ayyuka,a watan Oktoban da ya gabata a yayin da ya mika kasafin kudi na shekara ta 2020.

Labarai

Abinda ya sanya ‘yan adai-daita sahu janye shiga yajin aiki

Published

on

A yau jumu’a ne direbobin baburan adai-daita sahu na jihar Kano suka kudiri aniyar tafiya yajin aiki da kuma zanga-zanga, sakamakon harajin kudi har naira dubu ashirin da shida da hukumar KAROTA ta sanya musu.

Sai dai biyo bayan wani zaman sulhu da shugabannin kungiyoyin ‘yan adai-daitar sukayi da shugaban hukumar KAROTA an cimma matsaya, inda akayi yarjejeniyar cewa direbobin zasu biya naira dubu takwas-takwas kafin karshen watan disambar da muke ciki.

Tunda farko dai hukumar KAROTA ta kudiri aniyar rage yawan direbobin adai-daita sahun ne, ka sancewar sunyi yawa a gari fiye da kima, domin kuwa duk inda ka zaga, zaka hangi kalar ruwan dorawa irin ta baburan wadda kuma tayi kama da kayan sarki irin na jami’an Hukumar ta KAROTA.

Baya ga hakama dai hukumar KAROTA na zargin wasu daga direbobin na KAROTA na aikata wasu munanan laifuka.

Sai dai a karshe shuwagabannin ‘yan adai-daita sahun sun amince da janye yajin aikin da kuma zanga-zangar da suka shirya farawa a yau jumu’a, sai dai an jiyo wani tsagin kungiyoyin ‘yan adai-daita sahun na Kano na cewa suna nan akan bakansu, don haka basu gamsu da waccan maslaha ba kuma zasu tsunduma yajin aikin a yau.

Allah ya kyauta.

Labarai masu alaka:

Gwamanatin Kano za ta rage yawan baburan adaidaita sahu

Hukumar KAROTA ta nemi a kebe mata Naira biliyan guda

Continue Reading

Labarai

‘Yan sanda a Kano sun gargadi jama’a kan aikata laifi ranar bikin Maukibi

Published

on

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano gargadi al’umma, musamman bata gari da suke fakewa da lokacin taron jama’a domin aikata laifukan sara suka, da sauransu.

Cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ‘yan sanda ta jihar Kano DSP. Abdullahi Haruna Kiyawa ya rabawa manema labarai a daren yau, ya bayyana cewa rundunar ‘yan sanda ta shirya tsaf domin kula da shige da fice aranar Asabar mai zuwa da za’a gudanar da bikin maukibin waliyai da mabiya darikar Qadiriyya gabatarwa duk shekara a Kano.

DSP. Kiyawa ya bayyana cewa sunyi shiri na musamman domin zakulo wadanda suke fakewa da irin wadannan taruka su tayar da hankalin jama’a, a don haka suna gargadin al’umma dasu guji yin shigar banza, ko sanya kayan mata ko kuma yin wata shiga wadda ta saba da al’ada ko kuma addinin al’ummar jihar Kano.

Labarai masu alaka:

Rundunar ‘yan sandar jihar Kano ta sake ceto wani yaro a Anambra

Rundunar ‘yan sanda ta Kano ta yi holin masu yin garkuwa da mutane

Kazalika rundunar ‘yan sandan jihar Kano tayi shiri na musamman domin dakile masu ta’ammali da miyagun kwayoyi, da sara suka ko kwacen wayoyi da sauran laifuka a yayin gudanar da taron maukibi na bana.

Haka kuma rundunar ‘yan sandan jihar Kano na sanar da jama’a cewa har yanzu dokar nan tana nan ta haramta yin wani gangami ko zanga-zanga ko wani taron jama’a ba bisa ka’ida ba, kuma duk wanda ya karya wannan doka to babu shakka hukuma zatayi aiki akansa a cewar, kuma anyi hakan ne domin tabbatar da zaman lafiya a jihar Kano a cewar DSP. Kiyawa.

A karshe rundunar ‘yan sandan ta taya al’ummar musulmi murnar zagayowar wannan wata da fatan za’a kammala bukukuwa lafiya.

Labarai masu alaka:

‘Yan film sun karrama kwamishinan ‘yan sanda na jihar Kano

Jihar Kano ta sami sabon kwamishinan ‘yan sanda

Continue Reading

Labarai

Ma’aikatan lantarki sun koma bakin aiki

Published

on

Kungiyar ma’aikatan wutar lantarki ta kasa NUEE, ta janye yajin aikin sai baba ta gani da ta fara a jiya Laraba da nufin janyo hankalin gwamnatin tarayyar Najeriya kan hakkokin mambobinta.

Kungiyar dai ta sanar da janye yajin aikin ne da safiyar yau alhamis sakamakon wani zaman gaggawa da ta yi da jami’an gwamnatin tarayya.

Shugaban kungiyar ta NUEE na kasa kwamared Joe Ajaero ne ya tabbatar da janye yajin aikin ga manema labarai, yana mai cewa, sun tattauna matsalolin ma’aikatan sosai kuma gwamnatin tarayya ta yi alkawarin shawo kan matsalar.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa, shiga yajin aikin kungiyar ya biyo bayan karewar wa’adin kwanaki 21 da ku kungiyar ta baiwa ministan lantarki Saleh Mamman, domin duba bukatun mambobinta, inda kuma rashin sauraron su da ya yi ne ya sanya su fara yajin aikin.

Continue Reading

Now Streaming

Trending

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.