Labaran Kano
Hukumar korafe korafe na binciken Alkalan Kotun Majistret
Hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano, ta ce ta fara bincike kan zargin korafin cin hanci na wasu Alkalan Kotun Majistire uku anan Kano.
Hukumar a baya-bayan nan ta ce ta samu irin wannan korafe-korafe da dama kan Alkalan Majistire daga bangarorin al’umma.
Daraktan ayyuka na musamman na hukumar karbar korafe-korafe da hana cin hanci da rashawa ta jihar Kano Malam Usman Bello ya shaidawa jaridar solacebase game da almundahar da ake zargin alkalan sun tafka.
Rahotanni na nuni da cewa, akwai Alkalin Kotun Majistire ta 34 dake Rijiyar Zaki da aka cire shi aka sauya masa wurin aiki zuwa dakin ajiye karatu na babbar kotun jiha, kasancewar yawaitar korafe-korafe da ake samu akan sa.
Mun warware korafe-korafe masu dinbim yawa- Muhyi Magaji
Hukumomi sun rufe asibitin Maita a Kano
Mun kama Sarkin mayu na bogi-Muhiyi Magaji
Malam Usman Bello ya bayyana cewar an sanar da babban jojin Jihar Kano Justice Nura Sagir Umar game da binciken.
Wata majiya daga gidan gyaran hali dake cikin birnin Kano ta shaida cewa, galibin wadanda ke jiran shari’a a gidan sun shigo ne ta hannun Alkalin Majistiren Aminu Usman da aka fi sani da ‘Dino’.
Al’umma da dama ne dai suka yi ta nuna farin cikin su a Juma’ar da ta gabata, biyo bayan sauyawa lauyan majistiren wurin aiki da hukumomin suka yi.
A yayin da ake yi masa tambaya akan sauran Majistirorin biyu da ake ci gaba da bincika, daraktan hukumar hana karbar korafe-korafe da cin hanci da rashawa ta jihar Kano Malam Usman Bello ya ce shakka babu bayyana sunayen na su zai kawo tasgaro a sha’anin binciken na su.