KannyWood
Halin da ake ciki a Kannywood a wannan mako
A wannan makon babban labarin da ya mamaye masana’antar Kannywood shi ne zargin yin awon gaba da kudaden marayu da jarumi Yusuf Haruna wanda akafi sani da Baban Chinedu ya yiwa shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’ila Na’abba Afakallah.
Tun da farko dai, Baban Chinedu ya wallafa wani bidiyo a shafinsa na Instagram wanda aciki ya zargi Afakallahu da cewa bai isar da sakon tallafin kayan aure da gwamnan jihar Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya bayar ga iyalan marigayi Rabilu Musa Ibro a lokacin da za’ayi bikin ‘yar sa.
Har ila yau Baban Chinedu ya wallafa hoton wasu kayan daki, da tarin kayan abinci da Afakallahun ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar 19 ga watan Janairu na shekara ta 2018 dauke da rubutun cewa “Iyalan Ibro na godiya mai girma gwamna”.
Shima a nasa bangaren Adnan Musa Danlasan wanda dan uwa ne ga marigayi Rabilu Musa Ibro ya bayyana cewa gwamnatin Kano bata basu tallafi ba a yayin wancan aure na ‘yar marigayi Ibro.
Sai dai a ranar Talata, 18 ga watan Fabrairu 2020, yayin da ake tsaka da wannan dambarwa sai aka ci karo da wata takarda wadda shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Na’abba Afakallahu ya wallafa a shafin sa na Instagram.
Cikin takardar Lauyan Afakallahu mai suna Abdullahi Musa Karaye, tare da abokan aikin sa lauyoyin sun umarci Baban Chinedu da ya sauke bidiyon da ya saka a dukkan shafukansa sannan ya sake yin wani bidiyon na bayar da hakuri tare da karyata kan sa a cikin awa 24.
Bisa sharadin cewa matukar bai yi hakan ba, to tabbas za su gurfanar dashi a gaban kotu domin nemawa Afakallahu hakkinsa bisa zargin cewa Baban Chinedu ya bata masa suna.
Sai dai kwatsam Baban Chinedu ya kara sakin wani sabon bidiyon wanda ya kara yin zargi akan batun.
A wannan makon da muke ciki ne fitaccen kamfanin shirya fina-finan nan na FKD mallakar jarumi Ali Nuhu ya cika shekaru 20 cif da kafuwa.
Ali Nuhu yayi amfani da sunan mahaifiyar sa Fatima wajen kirkirar sunan kamfanin.
Fim na farko da kamfanin ya fara yi shi ne, “Sabani” wanda ya fito a watan Janairu na shekara ta 2000.
A wani labarin kuma wasu hotunan jaruma Saratu Gidado wadda akafi sani da Daso tare da yar shugaban kasa Zahra Buhari ya haifar da cece kuce a kafafan sada zumunta.
Al’umma da dama ne suka rika bayyana ra’yoyinsu akan hotunan wadanda suka yadu a wannan makon.
A ranar Asabar din da ta gabata ne matar Jarumin nan Mustapha Naburaska ta haifi ‘ya mace kamar yadda ya wallafa a shafinsa na dandalin sada zumunta na Instagram.
Masoyan jarumin sun rika aike masa da sakon fatan alkhairi.
A sakamakon taɓarɓarewar al’amura a masana’antar fina-finan Hausa, wani kwamiti da ‘yan fim ɗin su ka kafa ya ɗauri aniyar yin addu’o’i tare da azumi domin rokon Allah ya kawowa masana’antar dauki.
Fitaccen mawaƙi kuma jarumi Misbahu M. Ahmad da Salisu Officer ne su ka kafa wannan sabon kwamitin addu’a.
Misbahu M. Ahmad yayi jawabi mai tsawo acikin wani sakon sauti da yayi ya kuma aika dasu zuwa ga zaurukan ‘yan masana’antar, inda ya roke su kan su dage da addu’o’I da kuma yin azumi don agaji daga wurin ubangiji kan matsalolin dake kara addabar masana’antar, kamar yadda mujallar Film Magazine ta rawaito.
A wani labarin mai kama da wannan kuwa Shugaban ƙungiyar ƙwararrun masu shirya fina-finai ta ƙasa wato (MOPPAN), Dakta Ahmad Muhammad Sarari, ya yi kira ga dukkan ‘yan masana’antar shirya finafinan Hausa kan su tashi tsaye wajen yin addu’o’i domin ceto masana’antar daga halin da ta ke ciki.
Cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran kungiyar Malam Al-Amin Ciroma, ta ruwaito Dakta Sarari na cewa: “Lokaci ya yi da kowanne mai kishin masana’antar zai fito ya mara wa dukkan shirye- shiryen da ake yi don samun ci-gaba.
“Komawa ga Allah gami da ƙudirin alheri, su na daga cikin abin da ya kamata mu yi, domin su na daga cikin hanyoyin samar da nasarori a cikin kowanne lamarin.”
A nan kuma fitaccen mai bada umarnin nan Aminu Saira ya bayyana cea Babu inda dokar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta ce a kama mawaki ko jarumi, saboda ba su ke da hurumin sakin waka ko film a kasuwa ba.
Aminu Saira ya bayyana hakan ne ta cikin shirin RA’AYI RIGA na BBC HAUSA, a ranar jumu’a wanda ya maida hankali kan wutar da ta kunno kai a masana’antar Kannywood.
Tashar talabijin ta Arewa 24 ta sanar da cewa za a ci gaba da nuna sabon shirin ‘Kwana Casa’in’ zango na 3 a ranar 5 ga watan Afrilu na wannan shekarar ta 2020.
Cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na Facebook ya baiwa masoyan shirin damar bayyana ra’ayoyin su da kuma fatan da suke dashi a sabon zangon wasan kwaikwayon.
A wani labarin kuma a wannan makon ne jaruma Aisha Dan Kano ta cika shekaru hudu da rasuwa.
Idan zaku iya tunawa jarumar ta rasu a ranar 23 ga watan Fabrairu na shekara ta 2016, inda aka yi jana’izarta a unguwar Gwammaja layin Musa U.A.C dake nan Kano.
You must be logged in to post a comment Login