Labaran Wasanni
Za’a kece raini tsakanin Man City da Madrid
Wasa ne da zai dau hankalin yan kallo kwarai da gaske a fadin duniya musamman ma ga magoya bayan kungiyoyin biyu da masu sha’awar tamaula duba da yadda kungiyoyin ke da tasiri a gasar da kuma gasar kakar wasannin kasashen su , wato Ingila da Andalus (Spain ).
A bangare daya kuma duba da tasirin masu horrar da kungiyoyin wato Joseph Pep Guardiola na Manchester City, Zinedine Zidane na Real Madrid , da su kansu sun yi shuhura lokacin da suna tamaula da nasarorin da suka samu.
Kuma suna masu horas wa, inda suna da nasarori da dama wajen lashe kofuna ciki har da na Zakarun nahiyar turai a matsayin su na yan wasa da kuma masu horar wa.
Sai bangare na uku tasirin wasan ta hanyar yan Kwallon da ke cikin kungiyoyin guda biyu, ‘yan wasa irin su Kevin De Bruyne, Riyard Mahrez, Ilkay Gundogan, Sergio El Kun Aguero, Ederson, Benjamin Mendy da Raheem Sterling daga bangaren Manchester City suna ye ne da duk kungiyar data ji su ko zata fuskance su zata ji dar ba.
Yadda wasannin zakarun nahiyar Turai ke gudana
Rahoto : Nazari kan wasanni na gida tana ketare
Gwamnatin Kano za ta kashe sama da miliyan 98 a bangaren wasanni
In muka leka kungiyar Real Madrid , sunayen Luca Modric, Casemeiro, Kareem Benzema, Rafeal Varane, Toni Kroos, Isco Alarcon, sunaye da suke tamkar ihun Zaki ga dabbobi a ciki daji ta bangaren tsoratarwa.
Dangane da yadda wasa zai kaya , watakila za a iya tashi wasa 3-2 Manchester City tayi galaba akan Real Madrid a wasan farko.
You must be logged in to post a comment Login