Addini
A fara duban watan Rabi’ul-Awwal – Sarkin Musulmi

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya umarci al’umma da su fara duban watan Rabi’ul Awwal daga ranar Alhamis 7 ga watan Oktoban 2021.
Wannan na cikin wata sanarwa da fadar sarkin musulman ta fitar.
Sanarwar ta bayyana lambobin wayar da da za a sanar da kwamitin duban wata na fadar sarkin kamar haka: 08037157100 da 08035965322.
Sanarwar ta buƙaci al’umma da su gudanar da murnar haihuwar Manzon Allah SAW a cikinsa, kuma a cikinsa ne ya yi wafati.
You must be logged in to post a comment Login