Labarai
A hukunta masu hannu a gobarar ofishin Akanta na kasa-Joe Odumakin
Shugabar cibiyar kawo Canji, wato ‘center for change’ Dakta, Joe Okei- Odumakin, ta bukaci gwamnatin tarayya da ta gufanar da wadanda aka kama suna da hannu wajen gobarar da ta tashi a ofishin Akanta Janar na kasa.
Dakta , Joe Okel Odumakin ta bukaci hakan ne ta cikin sanararwar da ta fitar a birnin Lagos, in da tace ya zama wajibi a kama tare da gurfanar da wadanda suka haddasa gobarar.
Labarai masu alaka.
A Yanzu -Yanzu : gobara ta tashi a Ofishin akanta na kasa
Gobara ta lalata dukiyoyi masu yawa a Kano
Kazalika Odumakin ta nemi Gwamnatin tarayya da ta gudanar da bincike don gano musababin gobarar.
Har ila yau shugabar cibiyar ta ce kada Gwamnatin tarayya ta kyale batun gobarar ya tafi ba tare da an hukunta masu hannu a cikin laifin tashin ta ba.
A jiya Laraba gobarar ta tashi a ofishin Babban Akanta na kasa, wanda kawo yanzu haka ba’a san abinda ya haddasa ta ba.
You must be logged in to post a comment Login