Addini
A kullum muna ciyar da mutane dubu 75 abincin buda baki a Kano – Ganduje
Gwamnatin jihar Kano ta ce, tun bayan fara azumin watan Ramadan, a duk rana tana ciyar da mutane dubu 75 da abincin buda baki a kananan hukumomi 8 da ke cikin birnin Kano.
Mai taimakawa gwamnan Kano na musamman kan kafofin yada labarai na radio da talabijin, Abubakar Kofar-Naisa ne ya bayyana haka ga manema labarai.
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannunsa, da ya rabawa manema labarai, ta ce, akwai cibiyoyin rabon abinci akalla guda dari da hamsin a kananan hukumomi takwas da ke birnin Kano.
Abubakar Kofar Na’isa wanda shine jami’in yada labaran kwamitin kula da rabon abincin azumin na gwmanatin Kano, ya ce, tun bayan fara shirin a shekarar 2015, a duk shekara gwamnatin Kano tana kara adadain cibiyoyin rabon abincin don jama’a su amfana.
You must be logged in to post a comment Login