Labarai
Gwamnatin Kano ta sha alwashin magance matsalar ambaliya da zai-zayar ƙasa

Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za ta kammala aiwatar da manyan ayyukan magudanan ruwa da hanyoyi a yankunan da matsalar zaizayar ƙasa da ambaliya ke yi wa barazana, musamman a lokacin damina.
Kwamishinan Ma’aikatar Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ne ya bayyana hakan yayin wata ziyarar duba aikin gina hanya da magudanan ruwa daga Getsi zuwa Gayawa Bulbula da ya kai a safiyar Juma’a.
Da yake zantawa da manema labarai bayan duba aikin, Dakta Dahiru Muhammad Hashim ya yaba da ƙwazon injiniyoyi da sauran ma’aikatan da ke gudanar da aikin, inda ya ce suna aiki cikin sauri tare da kiyaye ingancin da ake buƙata.
Ya bayyana cewa aikin wani ɓangare ne na babban shirin gwamnati na inganta hanyoyin sufuri da magance matsalolin ambaliya a yankin, inda ya ƙunshi faɗaɗa babban magudanin ruwa da kuma gina gadoji guda biyar domin sauƙaƙa zirga-zirga da kare al’ummomin yankin daga illolin ambaliya.
Kwamishinan ya jaddada kudirin gwamnatin jihar na tabbatar da kammala ayyukan cikin lokaci domin al’ummar yankunan su ci gajiyar su, musamman a wannan lokaci da ake tunkarar damina.
You must be logged in to post a comment Login