Kiwon Lafiya
A tabbatar an kashe kudaden tallafin da ake samu ga harkokin lafiya – Buhari
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci ministan Lafiya da ya tabbatar da an amfana da gudummawar da asusun tallafawa kasashe zai bayar ga Najeriya na dala miliyan 890, cikin shekaru uku masu zuwa.
Shugaban Najeriyar ya ce asusun ya shirya bada tallafin ne ga Najeriya don ci gaba da yaki da cutar kanjamau, tarin fuka da Malaria.
Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne a wajen bikin kaddamar da tallafin dala miliyan 890, na shekarar 2021 da 2023, wanda kuma zai taimaka wajen karfafa ayyukan kiwon lafiya a kasar nan.
Muhammadu Buhari ya kuma ce Najeriya kasa ce da ke yaki da cin hanci da rashawa a don haka a kwai bukatar a tabbatar da an yi aiki da kudaden yadda ya kamata, musamman wajen dakile sabbin cututtukan da ke barazana ga al’umma.
You must be logged in to post a comment Login