Manyan Labarai
A wata ana haihuwar jarirai dubu daya a asibitin Murtala
A kowanne wata ana haifar jarirai da suka kai dubu daya a wata a asibitin Murtala dake nan Kano.
Wata likitar yara a asibitin koyarwa na Aminu Kano Dr Zubaida Farouk Ladan ce ta bayyana haka lokacin da take tattaunawa da filin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio.
Dr Zubaida tace a duk rana ana iya haifar jarirai dari a asibitin kwararru na Murtala Muhammad dake birnin na Kano.
Ta kara da cewa daga cikin abubuwan da ya kamata a duba domin inganta lafiyar jarirai ya hada da tsaftace guraran da ake ajiye su bayan an haife su.
Hukumomi sun rufe asibitin Maita a Kano
Gwamnatin Kano ta tuhumi shugaban asibitin Rimingado
Dr Zubaida ta kara da cewa a yanzu asibitin na Murtala na da gadajen kwantar da jarirai guda sha shida ne idan ana bukatar hakan da zarar an haife su.
Tace akwai wata cuta da ke samun jarirai da an haife su wanda ya kamata a duba da zarar masu karbar haihuwa sun karfi haihuwar jarirai.
Dr Zubaida Faruk tace rashin kwararrun masu karbar haihuwa na taimakawa kwarai da gaske wajen tabbatar da wasu cututtuka na jarirai.