Labarai
Abduljabbar ya aike wa Ganduje buƙatunsa kan Muƙabala
Malamin nan Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara ya ce, ya aike wa da Gwamna Ganduje buƙatunsa domin zaman muƙabala da malamai.
A wata sanarwa da malamin ya fitar cikin daren Lahadi ya ce, ya yaba wa Gwamnan Kano kan bashi dama domin tattaunawa da malamai game da ƙorafin da suka yi a kansa.
Malam Kabara ya ce, ya shirya tsaf kuma zai halarci zaman muƙabalar, da kuma bashi dama ya zo da litattafansa da kuma karatukansa.
Sai dai ya nemi a amince ya zo da wani mutum da zai lura da litattafansa da kayan karatunsa.
A ƙarshe ya ce, zai zo zaman da zuciya ɗaya kuma yana fatan suma ɗaya ɓangaren su zo da zuciya ɗaya.
A ɓangaren zauren haɗin kan malaman Kano kuwa, babban sakataren zauren Dr. Sa’id Ahmad Dukawa ya shaida wa wakilin mu Ado Sa’id Warawa cewa sun samu takardar umarni daga gwamnatin Kano wadda ta nemi su fitar da malaman da za a kara da su.
Labarai mai alaka:
Majalisa ta nemi Buhari ya mayar da Nasir Argungu kan mukamin sa
You must be logged in to post a comment Login