Siyasa
Abin da aka tattauna tsakanin Abdul’aziz Ganduje da Sanata Barau
Ɗan Gwamnan Kano Umar Ganduje ya kai wa Sanatan Kano ta Arewa Barau Jibrin ziyara.
A ranar Asabar ne hotunan ziyarar suka karaɗe kafafen sada zumunta, inda aka riƙa muhawara a kai.
Sanata Barau Jibrin dai na cikin manyan jiga-jigan tsagin Sanata Malam Shekarau, waɗanda suka shata layi da Gwamna Ganduje.
Me yasa Abdulaziz ya ziyarci Sanata Barau?
Freedom Radio ta tuntuɓi Alhaji Murtala Alasan Zainawa, Daraktan yaƙin neman zaɓen Sanatan wanda ya tabbatar da ziyarar.
Ya ce, “Abdul’aziz Ɗanmu ne kuma mutum ne mai mu’amala, ya zo wajen Sanata ne domin ya yi masa godiya, kan aikin ginin makarantar da ya bai wa mahaifiyarsa”.
Ya ci gaba da cewa “Sanata ya bai wa mahaifiyar Abdulaziz aikin ginin makaranta a garin Malam Madori, wanda ita kuma ta bai wa Abdul ɗin aiwatar da aikin”.
“Yanzu an kammala shi ya sa ya zo domin ya yi godiya da ƙara ƙarfafa zumunci a tsakani” a cewar Zainawa.
To ko wannan ziyarar na nufin Abdulaziz ya dawo tafiyar G7?
Zainawa ya ce, ba abin mamaki bane domin kaso mai yawa na jami’an Gwamnatin Kano suna tare da tsagin G7 a ɓoye, lokaci ne zai nuna.
You must be logged in to post a comment Login