Labarai
Abubuwan da ya kamata ku sa ni game da marigayi Hosni Mubarak
Tsohon Shugaban kasar Masar (Egypt) Hosni Mubarak ya rasu yau yana da shekaru 91.
Marigayi Hosni Mubarak, ya shafe shekaru 30, yana mulkin kasar ta Misra, tun bayan da ya gaji tsohon shugaban kasar Marigayi Anwar Sadat, da aka kashe a shekarar 1981, in da ya jagoranci kasar har zuwa shekara ta 2011, da gagarumin juyin juya hali na zanga-zanga mai taken ‘Arab Spring Revolution wanda ya kawo karshen mulkin sa bayan da sojoji suka hambar da gwamnatin sa.
Mubarak, ya shafe shekarun 29, yana jagorantar kasar da gudanar da al’amurran ta tare da manyan kusoshin gwamnatin sa wanda iyalan sa sun taka gagarumar rawa a ciki.
A shekarar 2011, jim kadan bayan hambarar da gwamnatin sa da soji sukayi, an zarge shi da gwamnatin sa da yin mulkin kama karya, tare da hada kai da jami’an tsaro wajen kashe masu zanga-zangar juyin juya halin canja gwamnatin ta sa, wanda hakan ya sa aka yi masa daurin talala a gidan kaso bayan samun sa da laifi.
Sai dai daga baya, kotu ta wanke shi daga zargin da akayi masa tare da sakin sa daga daurin, a watan Maris na shekarar 2017.
A watan Janairu bana Mubarak, ya yi fama da matsanan ciyar rashin lafiya data sa akayi masa tiyata.
Da safiyar yau ne tashar talabijin ta kasar Masar, ta bayyana rasuwar sa, inda a baya, shafin internet na Alwatan, ya bayyana cewa ya rasu ne a Asibitin Sojoji dake birnin Alkahira wato Cairo, inda dan sa Alaa Omar, ya ce an kwantar da Mahaifin nasu a na’urar taimakawa numfashi ta intensive care, tun Asabar din makon da ya gabata.
Tarihin marigayin Hosni Mubarak
An haifi tsohon shugaban a shekarar 1928, a garin Kafar Al Musaylah, wanda bayan tasowar sa ya shiga aikin Sojin sama na kasar, ya kuma yi shuhura a lokacin yakin da kasashen larabawa suka fafata da kasar Isra’ila da aka fi sani da “Arab-Israeli war” a shekarar 1973.
Ya bada gagarumar gudun mowa wajen, shiga tsakani da bada shawar wari wajen samar da zaman lafiya tsakanin kasar Isra’ila da Palasdinu.
Rikincin da ya barke a makociyar kasar Misra, Tunisia na juyin juya hali da ya tafi da gwamnatin tsohon shugaban kasar ta Tunisia Zainul Abidine Ben Ali, ya rura wutar zanga-zanga a kasar Misrah, data bukaci shugaba Mubarak ya sauka da ga kan mulki, a watan Janairun shekarar 2011.
Shugaba Mubarak, ya yi kokarin zama akan mulki amma hakan yaci tura wanda bayan zanga zangar kwana 18, ya sauka daga kan Mulki, inda Sojoji suka karbi kasar kafin daga baya aka shirya zaben da, marigayi Muhammad Morsi, ya zama shugaban kasar a shekarar 2012 zuwa 2013, shekarar da Janar Abdulfatah Al-Sisi, ya yi masa juyin mulki.
You must be logged in to post a comment Login