Labarai
Abuja:Gwamnonin Najeriya sun fara taron nazartar dokar baiwa kananan hukumomi ‘yanci
Gwamnonin kasar nan talatin da shida sun fara wani taro a birnin tarayya Abuja domin sake nazartar dokar bai wa kananan hukumomin ‘yancin sarrafa kudaden su
Rahotanni sun ce haka kuma ana saran gwamnonin za su tattauna batun shirin lafiya a matakin farko da sauran wasu lamura na harkokin kiwon lafiya.
Gwamnonin talatin da shida za su kuma tattauna game da inda aka kwana kan shirin ci gaban muradun karni na majalisar dinkin duniya, da sauyin yanayi da kuma makomar taron da suka yi da bankin raya kasashen afurka AfDB da kuma masu zuba jari da kasar China.
Yayin fara taron a jiya gwamnonin da suka halarta sun hada da: shugaban kungiyar gwamnonin Kayode Fayemi na jihar Ekiti da mataimakin sa da Aminu Waziri Tambuwal na jihar Sokoto da gwamnan Abia Okezie Ikpeazu da Umaru Fintiri na jihar Adamawa da kuma Udom Emmanuel na Akwa Ibom.
Haka kuma akwai gwamnan jihar Anambra Willie Obiano da Samuel Ortom na Benue da Bala Abdulkadir Muhammed na Bauchi da kuma Godwin Obaseki na jihar Edo.
Sauran sune: Ifeanyi Igwuanyi na jihar Enugu da Abdullahi Umar Ganduje na nan jihar Kano da Darius Ishaku na Taraba da Abubakar Badaru na jihar Jigawa da Ifeanyi Okowa na Delta da Emeka Ihedioha na jihar Imo da Seyin Makinde na jihar Oyo da Aminu Masari na jihar Katsina da Bello Matawalle na jihar Zamfara da Babagana Zulum na jihar Borno da kuma mataimakin gwamnan jihar Cross River Farfesa Ivira Esu.