Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Kano

Abun da ya sa na gurfanar da Ganduje a gaban kotu – Abba K. Yusuf

Published

on

Dan takarar gwamnan Kano a jam’iyyar PDP Abba Kabir Yusuf ya bayyana dalilan sa na gurfanar da gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje da wasu ‘yan kasuwa a gaban babbar kotun jiha.

Abba Kabir ya bayyana hakan ne, ta bakin lauyan sa, Bashir Tudunwuzirci, wanda ya ce, ya shigar da karar ne, bisa zargin mallakawa wasu ‘yan kasuwa gine-ginen gwamnati da al’ummar jihar Kano ke amfana da su.

Baya ga gwamnantin Kano da ‘yan kasuwar, Abba Kabir Yusuf ya kuma yi karar ma’aikatar ayyuka da gidaje da sufuri ta jiha da atoni janar kuma kwamishinan shari’a na Kano da kuma hukumar kula da filaye ta jiha.
Abba Kabir Yusuf ya zargi gwamnatin Jihar Kano da mallakawa wasu daidaikun mutane tsohon otal din Daula da yanzu haka ke karakashin kulawar jami’ar kimiyyar da fasaha ta garin Wudil da kuma filin tashar Shahuci, da ya ce hakan ya ci karo da tanadin dokokin kasar nan.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!