Coronavirus
Adadin masu Corona ya kai 342 a Kano
Gwamnatin jihar Kano ta tabbatar da cewa adadin wadanda suka kamu da cutar Covid-19 a jihar sun kai mutane 342.
A daren lahadinnan, ma’aikatar lafiya ta jihar Kano ta wallafa a shafinta na Twitter cewa an samu karin mutane 29 da sakamakon gwajinsu ya nuna cewa sun kamu da cutar ta Corona, wanda ya kai adadin masu cutar zuwa 342.
Ma’aikatar lafiya ta Kanon ta ce mutane 8 daga cikin wadanda suka kamu da cutar a Kano sun rasa ransu.
Yanzu haka dai jihar Kano ce ke mataki na biyu a jihar da tafi yawan masu dauke da cutar Covid-19 a Najeriya.
Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya ne cibiyar gwajin cutar Corona dake jihar Kano ta samu tsaiko saboda rashin kayan aiki, sai dai daga bisani an samar da kayan aiki sannan an kara samar da sabuwar cibiyar gwajin cutar ta biyu a Kano.
Ko a ranar Lahadinnan ma an bude sabuwar cibiyar gwajin cutar Corona ta tafi da gidanka, da gidauniyar Aliko Dangote ta samar a asibitin Muhammadu Buhari dake Giginyu a Kanon.
Sabuwar cibiyar dai za ta rika gwada mutane 400 a kullum, inda bayan sati guda kuma zata koma gwada mutane 1000 a kullum.
Har ila yau, idan zaku iya tunawa a ranar Asabar ne gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya amince da sassauta dokar kulle da zaman gidan a jihar a ranakun Litinin da Alhamis.
You must be logged in to post a comment Login