Coronavirus
Adadin masu dauke da Corona ya kai 1728 a Najeriya
Cibiyar dakile cutuka masu yaduwa ta kasa NCDC ta ce a ranar Laraba an samu karin mutane 196 da suka kamu da cutar Covid-19 a sassan Najeriya.
Cikin sanawar da NCDC ta wallafa a shafinta na Twitter a daren Larabar nan ta ce an samu karin ne daga jihohin Lagos inda aka samu karin mutane 87 sai Kano da ta samu karin mutane 24, Gombe ta samu karin mutum 18 sai Kaduna da aka samu karin mutum 17.
196 new cases of #COVID19 reported;
87-Lagos
24-Kano
18-Gombe
17-Kaduna
16-FCT
10-Katsina
8-Sokoto
7-Edo
6-Borno
1-Yobe
1-Ebonyi
1-AdamawaAs at 11:55pm 29th April- 1728 confirmed cases of #COVID19 reported in Nigeria.
Discharged: 307
Deaths: 51 pic.twitter.com/1ul1P8JvTH— NCDC (@NCDCgov) April 29, 2020
Birnin tarayya Abuja an samu karin mutum 16 sai Katsina da aka samu karin mutum 10, Sokoto ta samu karin mutum 8 yayin da jihar Edo ta samu karin mutum 7.
Jihar Borno an samu karin mutum 6, sai jihar Yobe da aka samu mutum 1, jihar Ebonyi da Adamawa ma an samu karin mutum guda-guda.
Har ila yau, NCDC ta ce yanzu haka adadin wadanda suka kamu da cutar a Najeriya sun Kai 1728 yayin da 307 suka warke sarai.
Guda 51 kuma suka rasa ransu sanadiyyar cutar.
Karin labarai:
Covid19: Badaru ya bada umarnin rufe karin kananan hukumomi hudu
You must be logged in to post a comment Login