Labarai
ASUU ta bai wa gwamnatin jihar Gombe wa’adin mako 2

Ƙungiyar Malaman jami’o’i ta kasa ASUU reshen Jami’ar Jihar Gombe, ta bai wa gwamnatin jihar wa’adin kwanaki 14 kan ta biya buƙatunta ko kuma ta tsunduma yajin aikin sai Baba ta gani.
Ƙungiyar ta ce, yajin aikin zai fara ne daga ranar 25 ga watannan da muke ciki na Agusta idan ba a warware matsalolin da ta gabatar ba.
Buƙatun sun haɗa da biyan basussukan alawus-alawus na malamai da biyan bashin mafi ƙarancin albashi, da kuma aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya ta kulla da ASUU a shekarar 2025.
You must be logged in to post a comment Login