Labarai
ADC ta zargi ICPC da kare wasu jami’an gwamnati a binciken PFIPC

Jam’iyyar African Democratic Congress, ADC, ta zargi Hukumar ICPC da kare wasu jami’an gwamnati a binciken badakalar da ake zargin ta shafi Presidential Foreign Investment Promotion Council, PFIPC.
Jam’iyyar ta ce rahoton wucin-gadin da ICPC ta fitar bai bayar da cikakkun amsoshi kan yadda wata hukuma da ake cewa ba ta da tushe a doka ta samu ofishi a Sakatariyar Gwamnatin Tarayya, tare da ma’aikata da kuma naira biliyan daya da digo uku a kasafin kudin shekarar 2026.
ADC ta ce ICPC ta mayar da hankali ne kan Darakta-Janar na PFIPC, Adeniyi Adeyemi, wanda ta bayar da shawarar gurfanar da shi, alhali akwai bukatar binciken yadda wasu hukumomi da jami’an gwamnati suka taimaka wajen gudanar da ayyukan majalisar.
Jam’iyyar ta kuma yi tambaya kan yadda PFIPC ta samu damar shiga kasafin kudin shekarar 2026, tana mai cewa irin wannan kasafi na bukatar takardu, amincewa da kuma sahalewar hukumomin gwamnati.
ADC ta bukaci ICPC ta wallafa cikakken rahoton binciken, tare da gano dukkan jami’an gwamnati da suka taimaka ko suka yi sakaci wajen faruwar lamarin.
Jam’iyyar ta ce bai kamata a takaita binciken ga mutum guda ba, tana mai cewa ya kamata a bi dukkan hujjoji har zuwa inda suka kai.
You must be logged in to post a comment Login