Connect with us

Labarai

ADC ta zargi kwamitin yakin neman zaben Tinubu na 2027

Published

on

Jam’iyyar ADC ta zargi gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da mayar da kwamitin yakin neman zabensa na 2027 tamkar “Cibiyar gyaran hali” ga wasu mutanen da ke fuskantar zarge-zargen cin hanci da rashawa.

 

Sakataren yada labaran jam’iyyar na kasa Bolaji Abdullahi ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar. 

 

ADC ta nuna damuwa kan shigar da tsohuwar ministar harkokin jinkai, Betta Edu, da tsohuwar shugabar NSITF, Ngozi Olejeme, cikin kwamitin yakin neman zaben.

 

Jam’iyyar ta bukaci gwamnatin tarayya ta bayyana halin da ake ciki game da zarge-zargen da suka shafi mutanen, tare da tambayar ko an kammala binciken da ake yi, ko kuma nadin nasu wata hanya ce ta kare ko yafewa wadanda ake zargi da aikata laifukan cin hanci.

 

ADC ta kuma ce zaben 2027 zai kasance wata dama ga ’yan Najeriya su tantance ayyukan gwamnatin Tinubu da yadda ta tafiyar da kasar a cikin shekaru uku na farko na mulkinta.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!