Connect with us

Labarai

Sojoji sun kama mai safarar kuɗi da kayayyaki ga ’yan bindiga a Zamfara

Published

on

Rundunar haɗin gwiwa ta Operation FANSAN YAMMA ta ce dakarunta sun kama wani mutum da ake zargi da taimaka wa ’yan bindiga wajen safarar kuɗi da kayayyaki a jihar Zamfara.

Rundunar ta ce an kama mutumin ne a ranar Juma’a a kusa da Maradun, yayin da sojoji ke gudanar da samame da sintiri a wasu ƙananan hukumomin jihar.

A cewar rundunar, wanda ake zargin mai suna Lawali Dan Alo, mai shekaru 35, yana ɗauke da naira miliyan 5 da dubu 302 da wayar hannu a lokacin da aka kama shi.

Binciken farko ya nuna cewa ana zargin ya kai kuɗin ne a madadin wani shugaban ’yan bindiga ga wani mutum mai suna Kasimu Garba, wanda daga bisani jami’an tsaron suka kama a gidansa.

A wani samame daban, rundunar ta ce dakarunta sun gano tare da lalata wani abin fashewa da aka dasa a kusa da ƙauyen Jabanda da ke ƙaramar hukumar Zurmi.

Sojojin sun kuma yi arangama da wasu ’yan bindiga a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Shinkafi, inda suka tilasta musu tserewa zuwa daji.

Rundunar ta ce bayan arangamar, dakarun sun gano babura uku, kayan sojoji da wasu kayayyaki da ake zargin ’yan bindigar suka bari a yayin da suke tserewa.

Rundunar ta ce Lawali Dan Alo da Kasimu Garba na hannun jami’an tsaro, yayin da ake ci gaba da bincike domin gano ƙarin bayanai kan zargin da ake musu.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!