Labarai
Kwamitin majalisar wakilai zai gurfanar da babban Akanatan Najeriya

Kwamitin da ke binciken kafa hukumar Bogi na majalisar wakilai zai gurfanar da babban Akanatan kasar nan Mista Shamsedeen Ogunjimi, a yau domin yi masa tambayoyi dangane da yadda aka fitarwa da hukumar kudi.
Kwamitin, karkashin jagorancin dan majalisa mai wakiltar kananan hukumomin Kanke, Kanam da Pankshin a Jihar Filato, Yusuf Gagdi, na binciken yadda hukumar Bogin ta samu ofis a harabar Babbar Sakatariyar Gwamnati da ke Abuja, tare da samun fiye da Naira biliyan Daya a cikin kasafin kudin shekarar 2026.
Binciken ya jawo hankalin jama’a bayan zargin cewa hukumar ta gudanar da ayyuka a cikin tsarin gwamnati duk da rashin sahihancin ta, lamarin da ya haifar da tambayoyi kan yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati da kuma tsarin sa ido kan hukumomi.
Ana sa ran Akanta Janar zai yi bayani kan yadda hukumar ta samu lambar kasafi wato (budget code), wadda ta ba ta damar shiga cikin kasafin kudin kasa duk da cece-kuce kan matsayinta a doka
You must be logged in to post a comment Login