Labarai
Rundunar sojin sama ta kasa ta kashe ’yan ta’addan ISWAP 36

Rundunar sojin sama ta kasa ta ce ta kashe ’yan ta’addan ISWAP 36 a wasu hare-haren sama da ta kai a kananan hukumomin Monguno da Biu na Jihar Borno.
Jami’in yada labarai na Operation Hadin Kai, Kyaftin Mohammed Goni, ya ce an kai hare-haren ne a dararen Juma’a da Asabar, bayan samun sahihan bayanan sirri da sa ido ta sama.
Ya ce a yankin Aduwa na Monguno, an kashe ’yan ta’adda 26 a hare-hare daban-daban, yayin da wasu 10 kuma aka kashe a yankin Buratai na karamar hukumar Biu.
Rundunar ta ce hare-haren sun taimaka wajen tarwatsa yunkurin ’yan ta’addan na sake haduwa da kuma gudanar da ayyukansu.
Ta kuma ce za a ci gaba da amfani da bayanan sirri da sa ido ta sama domin takaita zirga-zirgar ’yan ta’adda da kuma kara matsin lamba a kansu a yankin Tafkin Chadi.
You must be logged in to post a comment Login