Labarai
Shugaba Tinubu zai jagoranci babban taro kan ma’adinai

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, zai jagoranci wani babban taro kan ma’adinan da ake matuƙar buƙata a duniya, wanda za a gudanar a Manhattan, New York, ranar 21 ga Satumba 2026, a gefen taron Majalisar Ɗinkin Duniya.
Taron na Africa Minerals Strategy Group zai mayar da hankali ne kan yadda ƙasashen Afirka za su daina fitar da ma’adinansu a matsayin ɗanyen kaya kawai, su koma sarrafawa da ƙera kayayyaki a cikin nahiyar domin samun ƙarin darajar tattalin arziki. Afirka na da dumbin ma’adinai kamar lithium, copper, cobalt, graphite, manganese da rare earth elements.
Ana kuma sa ran shugabannin Afirka da masu zuba jari za su tattauna wani sabon tsarin haɗin gwiwa da zai taimaka wajen jawo jarin kuɗi, inganta sarrafa ma’adinai, samar da ababen more rayuwa da ƙarfafa matsayin Afirka a kasuwar ma’adinan duniya.
You must be logged in to post a comment Login