Labarai
Gwamnatin Kano ta haɗa kai da manyan makarantu wajen dashen bishiyoyi

Gwamnatin Jihar Kano ta haɗa kai da manyan makarantun gaba da sakandare wajen faɗaɗa shirin dashen bishiyoyi da kare muhalli.
Kwamishinan Albarkatun Ruwa, Muhalli da Sauyin Yanayi, Dakta Dahiru Muhammad Hashim, ya ƙaddamar da shirin a Kwalejin Musulunci da Ilimin Shari’a ta Mallam Aminu Kano, wato Legal.
Ya ce gwamnatin jihar na shirin dasa bishiyoyi miliyan goma a bana, bayan shirye-shiryen dasa miliyan ɗaya da miliyan uku da ta aiwatar a baya.
Ya ce bishiyoyi na taimakawa wajen tsaftace iska, rage zafin yanayi da yaƙi da zaizayar ƙasa.
A nata ɓangaren, makarantar ta nemi tallafin gwamnati wajen samar da ruwa, greenhouse da magungunan yaƙi da ƙwari da cututtukan amfanin gona.
Kwamishinan ya bayar da umarnin a haƙa wa makarantar rijiyar burtsatse, tare da cewa gwamnati na ci gaba da ƙoƙarin inganta samar da ruwa a jihar.
An kammala taron da dashen bishiyoyi tare da ɗalibai da mahukuntan makarantar.
You must be logged in to post a comment Login