Labarai
AFCON 2021: Na amince da matakin Rohr na saka ni a masu jiran ko ta kwana – Onuachu
Dan wasan Najeriya da ke taka leda a kungiyar kwallon kafa ta Genk, Paul Onuachu, ya nuna amincewarsa da matakin Gernot Rohr na ajiye shi a cikin masu jiran ko ta kwana a wasannin da Super Eagles za ta buga da Jamhoriyar Benin da Lesotho a watan Maris a cigaba da wasannin share fagen cin kofin Afirka na 2021.
A dai ranar 27 ga watan Maris ne Super Eagles za ta barje gumi da Squirrels a garin Port Novo dake a Jamhoriyar ta Benin, kafin daga bisa ta karbi bakuncin kungiyar Crocodiles ta kasar Lesotho bayan kwanaki 3.
Magoya baya da yawa ne suka yi zaton cewa Rohr zai saka Onuachu cikin tawagar ‘yan wasan da za su fafata a wasannin da ake tinkara ba a benci ba.
“Onuachu mai shekara 26 ya yi nasarar cin kwallaye 26 a wasanni 30 tare da taimakawa wajen jefa kwallo 3 a dukkan gasanni a wannan kakar wasan,” a cewar Jaridar Punch.
You must be logged in to post a comment Login