Labaran Wasanni
Afrobasket: Kungiyar D’Tigress ta fitar da sunayen ‘yan wasa 13
Mai horas da ‘yan wasan kwallon Kwando na Kasa D’Tigress Otis Hughley ya fitar da sunayen ‘yan wasa 13 da za su wakilci kasar nan a wasan kwallon Kwandon mata ta Afrika mai taken Afrobasket 2021.
Za’a fara gudanar da gasar a ranar Juma’a 17 zuwa 26 ga watan Satumbar da muke ciki ta shekarar 2021, inda za’a buga gasar a Birnin Yaounde dake kasar Cameroon.
Kungiyar ta, D’Tigress itake dauke da gasar inda ta dauka a shekarar 2017 da kuma 2019 a jere sun sauka a garin na Yaounde a jiya Talata.
Rashin daukar wasanni a matsayin sana’a shine matsalar Najeriya-Muhammad Abdullahi
A cikin wata sanarwa da hukumar kwallon Kwando ta Najeriya ta fitar ta ce sunayen ‘yan wasan sun hadar da; Adaora Elonu, Elizabeth Balogun, Promise Amukamara, Ezinne Kalu, Pallas kunayi- Akpanah Ifunanya Ibekwe, Amy Okonkwo.
Sauran sun hadar da; Oderah Chidom, Victoria Macaulay, Nicole Enabosi, Sarah Ogoke, Murjanstu Musa da kuma Nkem Uwa Akaraiwe.
D’Tigress dai tana rukuni na B a gasar inda za ta yi wasa da kasar Angola da Mozambique.
You must be logged in to post a comment Login