Connect with us

Labarai

Ahmad Musa ya raba gari da kungiyar Al Nassr ta Saudia

Published

on

Kyaftin din kungiyar Kwallon kafa ta kasa Super Eagles Ahmed Musa , ya raba gari da kungiyar sa ta Al Nassr dake kasar Saudi Arabia , bayan shafe shekaru biyu a kungiyar.

Ahmad Musa ,wanda ya koma kungiyar a shekarar 2018 daga Leicester City , akan Kwantiragin shekaru hudu , ya sanar da barin kungiyar duk da ragowar Kwantiragin shekaru biyu da suka rage a yarjejeniyar sa da kungiyar.

Ita ma kungiyar ta Al Nassr, ta sanar da tafiyar dan wasan a shafinta na Twitter tare da cewa “Muna godiya Shahon Najeriya , muna maka fatan alheri a gaba”.

Sanarwar dai na zuwa ne , bayan da dan wasan mai shekaru 28, ya musanta labarin barin kungiyar a baya -bayan nan.

Ana Alakanta dan wasan da komawa tawagar Fenerbahce ta kasar Turkiyya (Turkey ).

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!