Labaran Wasanni
Ahmad Musa ya taimakawa kungiyar sa ta Fatih Karagumruk wajen doke Istanbul Basaksehir

Kyaftin din kungiyar kwallon kafa ta kasa Super Eagles Ahmed Musa ya tallafa an zura kwallo a wasan da kungiyarsa ta Fatih Karagumruk ta samu nasara akan Istanbul Basaksehir da ci 3-1 a gasar Super Lig ta kasar Turkiyya.
An buga wasan dai a ranar Juma’a 1 ga watan Oktobar shekarar da muke ciki ta 2021.
Ahmad Musa, ya taimaka wajen bawa dan wasa Andrea Bertolacci kwallon da ya sa a raga ta biyu a wasan.
Mai shekaru 28 Ahmad Musa, ya zura kwallo guda a sabuwar kungiyar da ya koma a kakar wasannin da aka fara ta shekarar 2021/2022.
Kungiyar kwallon kafa ta Karagumruk dai na mataki na biyar da maki 13 a wasanni takwasa da ta buga a gasar.
You must be logged in to post a comment Login