Labarai
Aikin layin dogo daga Najeriya zuwa Maradi ya kai kaso 60- Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Tarayya ta ce aikin layin dogon da ya tashi daga jihohin Kaduna da Jigawa da Katsina zuwa Kano ya wuce birnin Maradi da ke jamhuriyar Nijar, ya kai kashi 60 cikin 100.
Ali Bukar guda cikin Injiniyan Ma’aikatar Sufuri na kasar nan da ke kula da Sashe na Biyu na aikin, ne ya bayyana hakan a lokacin ziyarar duba aikin da tawagar ‘yan jarida ta shugaban kasa ta kai a Jigawa.
Tawagar karkashin jagorancin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da sadarwa, Sunday Dare ya ce nan bada jimawa ba za’a iya kammala aikin.
You must be logged in to post a comment Login