Connect with us

Labarai

Gwamna Abba zai rantsar da Murtala Garo a matsayin mataimakinsa

Published

on

Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Yusuf, zai rantsar da sabon mataimakinsa Murtala Sule Garo, a yau Talata,

 

Za a gudanar da bikin rantsuwar ne a dakin taro na Coronation Hall da ke gidan gwamnati da ƙarfe 11:00 na safe.

 

A wata sanarwa da mai bai wa gwamnan shawara kan harkokin yada labarai, Ibrahim Adam, ta tabbatar da cewa an shirya taron tare da gayyatar manyan ‘yan siyasa, masu ruwa da tsaki, da jama’a domin halarta wannan muhimmin lamari na siyasa a jihar.

 

Wannan dai na zuwa ne bayan tantancewar da majalisar dokokin jihar ta Kano ta yi wa Murtala Sule Garo tun bayan da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya aike mata da sunan sa.

 

Haka dai ya biyo bayan aije aiki da tsohon mataimakin gwamnan Comrade Aminu Abdussalam Gwarzo Murabus ya yi sakamakon raba gari da gwamnan Kano ya yi da su zuwa jam’iyyar APC mai mulkin kasa

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!