Labarai
Akwai bukatar karin kungiyoyin tsaro a Kano
Wata kungiya mai fafutukar tabbatar da tsaro mai suna Mafita ta bayyana cewa jami’an tsaron da kasar nan su kadai ba za su wadatar da kasar nan ba wajen magance matsalolin tsaron da ake fuskanta.
Shugaban kungiyar reshen Jihar Kano Kwamared Sani El- Mansur ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan Freedom Radio, wanda ya tattaunawa kan harkokin da suka shafi tsaro a kasar nan.
Sani El-Mansur ya kara da cewa matsalar tsaro da aka samu ce ta sanya su kafa wannnan kungiya ta jami’an tsaron, don bayar da ta su gudunmawa ta hanyar tallafawa jami’an tsaro wajen gudanar da ayyukansu.
LABARAI MASU ALAKA
Anyi kira ga shugaba Buhari da ya kawo karshen matsalar tsaro
Kano ba ta bukatar kafa rundunar tsaro -Ganduje
Rufe wajan hakar ma’adanai a jihar Kebbi zai taimaka wajan rashin tsaro
A na ta bangaren daya daga cikin jami’an kungiyar Malama Aisha Muhammad Jalo da ta kasance cikin shirin, ta bayyana cewar yanzu haka banagaren mata na kungiyar ya sanya idanu a kan yadda yaya mata ke fuskantar matsalar shaye-shaye, inda kungiyar ke kokarin ganin an samu sauki ta a bangaren.
Bakin sun kuma bukaci al’ummar gari da su kasance masu sanya idanu a kan jama’ar da ke shige da fice a Unguwanninsu, tare da kai rahoton duk wanda ba su aminta da shi ba, don ganin an samar da tsaro a tsakanin al’ummar kasar nan.
You must be logged in to post a comment Login