Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Akwai bukatar sabbin masu horaswa 11 da aka nada su ciyar da kungiyoyin wasannin Najeriya gaba – Moukhtar

Published

on

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta birnin tarayya Abuja Abba Moukhtar Muhammad, ya nuna gamsuwarsa bisa nadin da hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta yiwa wasu masu horas da harkokin wasanni a Abuja su 11 a matsayin masu horas da rukunin kungiyoyin wasanni a kasar nan.

Abba Moukhtar Muhammad ya nuna jin dadinsa bisa wannan nadi da NFF ta yi ga masu horaswar daga kungiyoyi mabambanta.
A farkon makon da ya gabata ne hukumar kwallon kafa ta kasa NFF ta sanar da nadin sabbabin masu horaswar da suka hada da kungiyoyin maza da na mata.

Har ila Moukhtar Muhammad ya kara da cewa, wannan nadi na nuni da yadda NFF ke da kwarin guiwa ga sababbin masu horaswar.

“Wanan aikin kasa da aka bayar muna da kwarin guiwa ga masu horaswarmu za su iya kokarinsu dan ganin sun fita kunya duba da kwarewarsu da kishin kasa a tare da su, muna godiya ga NFF da take baiwa bangaren”.
“Ina kara yin kira ga wadannan sabbin masu horaswar da su gudanar da aikinsu cikin jajircewa da kwarewa”, a cewar Abba Moukhtar Muhammad.

Ladan Bosso dai shi ne aka baiwa jagorancin ‘yan wasan kasar nan maza ‘yan kasa da shekaru 20 sai kuma Christopher Dan Juma da zai jagoranci mata ‘yan kasa da shekaru 20, inda kuma Bankole Olowookere zai jagoranci mata ‘yan kasa da shekaru 17.
Haka zalika Fatai Amoo shi ne zai jagoranci maza ‘yan kasa da shekaru 17 inda kuma Omoniyi Haruna IIerika Usman zai jagoranci maza ‘yan kasa da shekaru 15.

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta birnin tarayya Abujan ya kuma bukaci Gwamnati da sauran masu ruwa da tsaki wajen ci gaba da baiwa matasan dake bangaren goyon baya, don samar da zakakuran ‘yan wasa da ka iya wakiltar kasar a bangarorin wasanni.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!