Labarai
Akwai bukatar sauya salon yaki da rashawa a Najeriya – Osinbajo
Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayyana cewa akwai bukatar Najeriya ta canja salon yadda take fuskantar yaki da cin hanci da rashawa a kasar.
Mataimakin shugaban kasa Osinbajo ya yi wannan bayani ne a ranar Talata wajen bikin yaki da cin hanci da rashawa da sauran laifukan da suka dangance su a yankin Afirka karo na 20 da aka gudanar ta intanet.
Bikin na bana da aka yiwa taken, ‘Sabbin dabarun magance cin hanci da kuma harkokin kudi ba bisa ka’ida ba’ ya zo ne a dai-dai lokacin da ake gudanar da bincike kan shugaban hukumar yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa, Ibrahim Magu kan zargin rashawa.
Ya ce babu wani siddabarun da za a iya yi don kawo karshen cin hanci da rashawa da kuma batar da sawun kudaden haram ko kuma kwato kadarorin da aka mallaka da kudin da aka samu ta hanyar cin hanci da rashawa.
Osinbajo ya ce abin yi kawai shine a dage da yin aiki tukuru tare da jajircewa sai an kai ga nasarar magance matsalar.
Ya kara da cewa dole ne a tabbatar da cewa an mayar da harkar cin hanci da rashawa abu mai matukar tsadar gaske ga dukkan wadanda ke da alaka da shi tare kuma da aikewa da kakkausan sako ga irinsu cewa harkar rashawa fa ba riba a cikinta.
You must be logged in to post a comment Login