Labarai
Akwai haramtattun makamai miliyan 6 a hannun jama’a a Najeriya – Abdussalam
Tsohon shugaban kasar nan na mulkin soji Janar Abdussalami Abubakar, ya alakanta rashin tsaron dake addabar kasar nan a yanzu da yawaitar makamai ba bisa ka’ida ba a hannun jama’a, wanda yawan su sun kai sama da miliyan shida.
Abduslami Abubakar, wanda yake shugaban kwamitin zaman lafiya na kasa (NPC),ya bayyana hakan ne jiya a Abuja lokacin da ya ke jawabi wajen taron tattaunawa na masu ruwa da tsaki akan harkokin tsaro.
Ya ce a yanzu haka, yawaitar makaman a hannun ‘yan ta’adda ya ta’azzara aiyyukan ‘yan ta’adda da kuma sanadin kashe al’ummar kasar nan sama da mutum 80,000.
Taron ya samu halartar , sarakunan gargajiya da suka hada da mai Alfarma sarkin Musulmi Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, da shugaban Cocin Katolika shiyyar Abuja, John Cardinal Onaiyekan, sai gwamnan jihar Ekiti Kayode Fayemi, dana Filato, Simon Lalong da shugabannin ‘yan kasuwa karkashin jagorancin Aliko Dangote.
You must be logged in to post a comment Login