Labarai
Akwai karancin ilimin harkar fim ga masu shirya fina-finai
Hukumar da ke lura da harkokin sadarwa ta kasa NCC ta sha alwashin lalubo hanyar da za’a saukaka kudin da ake cira ga masu amfani da data na internet domin gudanar da sana’oin su cikin sauki.
Daraktar tsare-tsare a hukumar ta NCC Muhammad Chuboado Babjika ne ya bayyana haka a yayin wani taron karawa juna sani tsakanin masu shirya- fina-finai da yan jaridu da aka shirya a Kano.
Muhammad Chubado Babajiki darakta a hukumar da ke lura da harkokin sadarwa wato NCC ya ce rashin kyakyawar alaka abin mamamki ne a tsakanin masana’antar shirya fina-finai da hukumar da ke lura da harkokin sadarwa duk kuwa da cewar dukkanin fannonin na kokarin isar da sako.
Muhammad Chubado ya ce hukumarsa ke da alhakin ba da rijista mussamam ga wadanda suke shirya fina-finai suke kuma dora su a kafar internet, a don haka dole a dama da hukumar NCC.
ya kara da cewar, suna tantance ire-iren wadannan fina-finai ne ta hanyar basu lasisi kuma kafin a basu wannan lasisi sai an nusar da su cewar a dole ne su bada fina-finan su domin a tantance kafin su fitar da wadannan fina-finan.
Har ila yau Dandali ya tambaye shi ina atun saukaka masu sana’ar fina-finai musammam ma ta kafar internet sai ya ce suna aiki akan haka domin ganin an saukakawa masu amfani da network a nan kusa ba da jimawa ba.
Ya ce a yanzun haka suna nazari na saukakawa da zasu baiwa kamfanonin da suke samar da data domin samun saukin aiki da ya dangance sadarwa.
Daga yake jawabi a yayin taron shugaban Moving Image Abdulkarim Muhammad ya ce masu shirya fina-finan a nan Arewacin kasar nan na da wuyar sha’ani sakamakon rashin baiwa wannan harkar muhimmanci ga Shirin na karawa wa juna sani musammam a fagen shirya fina-finai a duk inda ake shirya shi.
Sakamakon mafi yawan masu shirya wannan fina-finai basu da wata masaniya ga harkar fina-finai ko gudun kada a nuna gazawarsu a fina-finan da suke shiryawa.