Kiwon Lafiya
Akwai sauran rina a kaba, a yaki da miyagun ‘kwayoyi a Kano – inji ‘Yan Magani
Kungiyar masu sayar da magunguna a nan Kano ta ce, hukumomin dake yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi a Kano, na fuskantar karancin ma’aikata da kuma kayan aiki, wanda zai basu damar yakar ta’ammali da miyagun kwayoyin a tsakanin jama’a.
Shugaban kungiyar Alhaji Hussaini Labaran Zakari ne ya bayyana hakan ta cikin shirin “Duniyar mu a yau” na tashar Freedom Radio Kano, a ranar Litinin, yana mai cewar akwai bukatar gwamnati ta tabbatar ta wadata ma’aikatan hukumomin dake yaki da fataucin miyagun kwayoyi da kayan aiki.
Alhaji Hussaini Zakari ya ce, kungiyar su za ta baiwa hukumomin hadin kai wajen ganin an bankado gurbatattun ‘yan kasuwar dake sayar da miyagun kwayoyi.
Karin labarai:
Hukumar KAROTA ta cafke miyagun kwayoyi a Kano
NDLEA ta kama masu fataucin miyagun kwayoyi a Kano
A nasa bangaren wani kwararre a fannin kimiyyar harhada magunguna Ghali Sule, wanda ya kasance a cikin shirin, ya shawarci al’umma da su rika kula sosai da kwanan watan duk wani magani ko kayan masarufin da zasu siya, kasancewar amfani da gurbatattun kayan na haifar da illa matuka.
Wakiliyar mu Maryam Saleh Yusuf da ta bibiyi shirin ta rawaito mana cewa dukkan bakin sun yi kira ga jama’a da su zubar da al’adar nan ta neman arha wajen siyan magunguna, domin gujewa fadawa amfani da gurbatattun magunguna da ka iya cutar da lafiya.
You must be logged in to post a comment Login