Labaran Kano
Akwai tasgaro a takardar sammacin da aka aiko min – Baban Chinedu
Jarumin fina-finan Hausar nan Haruna Yusuf wanda aka fi sani da Baban Chinedu ya ce akwai tasgaro cikin sammacin kotu da aka aike masa, na shari’a tsakanin sa da shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Isma’il Na’abba Afakallahu.
A tattaunawar sa da Freedom Radio Baban Chinedu yace cikin kunshin tuhumar da aka aike daga kotun shari’ar musulunci ba a bayyana masa dalilin gayyatar tasa ba.
“Ba a fadi laifi ko korafin da ake tuhuma ta ba, an gayyace ni ne kawai ajikin takardar” a cewar sa.
Jarumin ya kara da cewa a yanzu haka yana cigaba da magana da lauyoyin sa, kan yadda za su tunkari shari’ar.
Karin labarai:
Kotu ta aikewa Baban Chinedu sammaci kan zargin Afakallah
Tabbas Afakallahu na kokari wajen tsaftace Kannywood –Kamaye
A jiya Alhamis ne kotun shari’ar musulunci dake Hausawa a nan Kano ta aikewa Baban Chinedu sammacin bisa korafin da shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ya shigar a kasa wanda ba a bayyana ba tuhumar ba ajikin takardar.
Idan zaku iya tunawa dai a kwanakin baya ne, Baban Chinedu ya zargi shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Afakallahu da yin rub da ciki da wasu kude da yace gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ya bayar don yin kayan aure ga ‘yar marigayi Rabilu Musa Ibro.
Sai dai Isma’il Na’abba Afakallahu ya bada wa’adin awanni ashirin da hudu ga Baban Chinedu kan ya janye wannan zargi ko kuma su hadu a kotu.
You must be logged in to post a comment Login