Labaran Wasanni
Akwai yiwuwar hana ‘yan wasan da ba a yiwa rigakafin Corona ba buga Kofin Duniya
Mahukuntan kasar Qatar na ci gaba da duba yiwuwar saka yin ragakafin Corona ya zama tilas ga ‘yan wasan da za su halarci kasar don buga gasar cin Kofin Duniya na 2022.
A wani rahoto da Jaridar The Athletic ta Ruwaito , ya tabbatar da cewar kasar ba za ta bar dukkan wani dan wasa shiga kasar ba matukar ba ayi masa Rigakafin ba.
Manyan kungiyoyin wasanni su rinka tallafawa kanana-Sarkin Kano
Sai dai idan hukuncin ya tabbata, hakan ka iya kawo rudani tare da rasa wasu zakakurarrun ‘yan wasa da za su halarci gasar , kasancewar wasu da dama basu yarda da ayi musu Allurar Rigakafin ba.
A baya baya nan dan wasan tawagar Arsenal Granit Xhaka , ya ki Amincewa da ayi masa Rigakafin , tare da mai tsaron gida na Newcastle United Karl Darlow , duk da fama da cutar Corona da ya yi jinya da ita shi Darlow.
Kasar ta Qatar na shirin fara gwada yin Rigakafin ga ‘yan wasan da za su fafata a gasar Kofin Larabawa na Arab Cup, da za’a Fara a ranar 30 ga watan Nuwamba na 2021.
Samun nasarar shirin a gasar ta kofin na Larabawan , shi zai bada dama ga kasar ta Qatar ta aiwatar da manufar ta ga ‘yan Wasa, ‘yan kallo da jami’an da za su halarci gasar ko kuma akasin haka.
You must be logged in to post a comment Login