Kasuwanci
Akwai yiwuwar janye yajin aikin kungiyar masu safarar kayan abinci zuwa kudu
Hadaddiyar kungiyar masu safarar kayan abinci da dabbobi zuwa kudancin Najeriya ta amince ta janye yajin aikin da ta shiga a makonnan.
Kungiyar ta amince da janye yajin aikin ne sakamakon shiga tsakanin da wasu gwamnonin kasar su ka yi a wata ganawa ta musamman a Abuja.
Haraji: Gamayyar kungiyoyin masu Abinci da dillalan Shanu za su tsunduma yajin aiki
Idan dai za a iya tunawa kungiyar ta shiga yajin aikin ne kan abinda ta kira cin zarafi da kuma kashe mambobinta da ake yi.
You must be logged in to post a comment Login