Labarai
Akwai yiwuwar samun ambaliyar ruwa a wannan shekarar – NIHSA
Ma’aikatar albarkantun ruwa ta Najeriya ta yi hasashen samun ambaliyar ruwa a wannan shekarar ta 2021.
Shugaban hukumar NIHSA mai kula da harkokin ruwa da kuma muhalli, Injiniya Nze Clement Onyeaso, ne ya tabbatar da haka yayin wata zantawa da manema labarai a Abuja.
Clement, ya ce a cikin rahoton hasashen da hukumar ta yi a baya-bayan nan, jihohin Kaduna da Lagos da Borno da Nasarawa ne aka samu ambaliyar sakamakon mamakon ruwan sama.
Sauran jihohin sun hadar da Anambra da Kwara da Rivers da Enugu da Abia sai kuma jihar Ondo.
Nze, ya gargadi jihohin da ke kusa da kogunan Niger da kuma Benue da su zama cikin shiri don akwai yiwuwar samun ambaliya nan gaba kadan.
You must be logged in to post a comment Login