Labaran Wasanni
Al Ahly SC ta hana Percy Tau zuwa wasan Afirka ta Kudu

Kungiyar Kwallon kafa ta Al Ahly SC, ta hana dan wasan gaba na kasar Afirka ta Kudu , Percy Tau zuwa wasan da kasar sa zata fafata na neman shiga gasar kofin Duniya.
A wata sanarwa da tawagar ta fitar a shafinta na Internet , tawagar ta ce ba zata bar dan wasan ba kasancewar yana jinyar rauni.
Al Ahly SC , ta tabbatar dacewar dan wasan zai cigaba da murmurewa tare da karbar Kulawa daga wajen Likitoci , don haka ba zai samu damar wakiltar kasar ba a wasanni da zata buga guda Biyu, a watan Oktoba.
You must be logged in to post a comment Login