Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Mariri Market Cup: Layin Aminu na Gwagwa ya yi rashin nasara a hannun Layin Auwalu Ragabza

Published

on

A Ci gaba da gasar cin kofin Mariri Cola Nut Market Cup, da ake kira da Chairman Cup, a wasan da aka buga yau Juma’a 24 ga watan Satumbar shekarar 2021, tsakanin kungiyar kwallon kafar Layin Auwalu Ragabza da Layin Aminu Na Gwagwa.

Layin Aminu na Gwagwa ya yi rashin nasara a hannun Layin Auwalu Ragabza da ci 4-2.

Dan wasan Layin Auwalu Ragabza Sina ne ya fara zura kwallo a mintuna na 15 da fara wasan ya kuma kara a mintuna na 53, wanda hakan ya bashi damar cin kwallaye 2, sai kuma Mubarak Tiago shima da ya ci tasa a mintuna na 54 inda Abbatiyo ya kara a mintuna na 60, hakan ya bawa Layin Auwalu Ragabza damar cin kwallaye 4 a raga.

A bangaren layin Aminu Na Gwagwa kuwa, dan wasa Umar Zalla ne ya ci kwallo a mintuna na 26 da fara wasan, kafin daga bisani Abdul ya ci tasa shima a mintuna na 50, hakan ya bawa Layin Aminu Na gwagwa damar cin kwallaye 2 a zare.

An dai take wasan da misalin karfe 4 na yammacin ranar ta Juma’a, a filin wasa na makarantar Sakandaren Mariri.

A ranar Lahadi 26 ga watan na Satumba za’a ci gaba da gasar cin kofin na Mariri Cola Nut Market da ake kira da Chairman Cup tsakanin FC Tasha da Layin Sabo Currency duk a kasuwar ta Mariri.

Wasan da za’a take da misalin karfe 4 da rabi na ranar a filin Sakandaren na Mariri.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!