Labaran Wasanni
Alkalin wasa Matthias Jollenbeck ya tsaida wasa domin dan wasa Moussa ya yi buda baki
Dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Mainz 05 Moussa Niakhate ya godewa alkalin wasa Matthias Jollenbeck bisa tsaida wasa da yayi domin bashi damar yin buda baki ana tsaka da wasan da suka fafata da Augsburg a filin wasa na WWK a gasar Bundesliga.
Karawar da ta gudana a ranar Litinin 11 ga Afrilun da muke ciki, lamarin da ya kasance irinsa na farko da wani alkalin wasa a kasar Jamus ya bawa dan wasa damar yin buda baki a watan Ramadan.
A minti na 65 ne dai alkalin wasan ya dakatar da wasan da ke gudana tsakanin Mainz’s da Augsburg domin bawa Niakhate damar yin buda baki.
Na’urorin dukar hoto mai motsi sun dauki lokacin da a ka kyale dan wasan bayan Mainz domin ya samu abin da zai sa a bakinsa a yanayin sauri, wanda hakan ya dadada wa yan kallo su ka rika yin shewa da tafi a benayen filin wasan.
A na tsayar da wasan mai tsaron gida na Mainz, Jeffrey Gouweleeuw ya garzayo da gudu ya mikawa Niakhat dan kasar Faransa Musulmi robar ruwar lema domin ya jika makoshinsa.
Ana tsaka da haka ne bayan ya kammala shan ruwan da lemon , ya jefa robar bayan fili, inda ya garzaya wajen alkalin wasa ya mika masa hannu su ka tafa, domin nuna farin ciki da damar da ya bashi.
Wasan dai an tashi Augsburg tayi nasara akan Mainz O5 da ci 2-1, kwallayen da ‘yan wasa Gouweleeuw da Ruben Vargas da Silvan Widmer suka zura a wasan.
Zuwa yanzu tuni hotuna suka mamaye kafafen sada zumunta inda su ke nuna lokacin da aka dakatar da wasan gasar ta Bundesliga na wucin gadi tsakanin Ausburg da Mainz don bawa Niakhat damar ya sha ruwa
*Waiwaye*
Ko a kakar wasannin da ta gabata ma an taba yin irin haka a gasar Firrimiya ta kasar Ingila.
Inda alkalan wasanni a gasar Firimiya ya tsayar da wasan da Leicester City ta fafata da hakan ya bawa dan wasan bayanta Wisley Fofana damar yin buda baki.
Haka kuma ‘yan wasa irin su Paul Pogba, Aboubacar Kyoteh, Sadio Mane sun samu damar yin buda baki a lokacin da suke fafatawa kungiyoyinsu wasanni.
You must be logged in to post a comment Login