Labarai
Allah ya yi wa Alhaji Musa Gwadabe Rasuwa
Allah ya yi wa daya daga cikin jiga-jigan dattijan siyasar jihar Kano Alhaji Musa Gwadabe Rasuwa.
Rahotonni sun bayyana cewa, marigayin ya rasu ne a cikin daren jiya Talata a Kano bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 91 a duniya, inda ya bar mata da ƴaƴa da jikoki da dama
Alhaji Musa Gwadabe ya kasance a matsayin Minista lokacin mulkin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo daga shekarar 1999 zuwa 2003, kuma Sakataren gwamnatin jihar Kano zamanin mulkin Sabo Bakin Zuwo.
Haka kuma har zuwa rasuwarsa, ya kasance mamba a jam’iyyar APC kuma shugaban shugaban gudanarwar hukumar ITF.
Za ai jana’izarsa da karfe 2:00 na rana, a gidansa da ke Maiduguri road a jihar Kano.
You must be logged in to post a comment Login