Labarai
Al’umma ke gaza bamu damar cikakken bincike – NBA
Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano NBA ta bayyana damuwarta bisa yadda al’umma ke gaza ba su damar yin cikakken bincike a yayin da ake tsaka da gudanar da wata shari’a.
Shugaban kungiyar na Jihar Kano Barista Aminu Sani Gadanya ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala shirin Barka da Hantsi na nan tashar Freedom Radio.
Barista Gadanya ya ce, kungiyarsu ta shiga a dama da ita a fannin shari’ar, wadanda ba za su iya daukar lauyan da zai tsaya musu a shari’a ba, sai dai akwai bukatar mutane su kara fahimtar yadda shari’a ta ke tare da bayar da bayanan sosai kamar yadda ake bukata.
A na sa bangaren sakataren kungiyar Barsita Haruna Salihu Zakariyya, ya ce tun bayan rantsar da su a matsayin sabbin shugabannin kungiyar sun tsara ayyukan da za su bunkasa kungiyar da kuma ciyar da bangaren shari’a gaba.
Bakin biyu sun bukaci al’ummar jihar Kano da su fahimci ayyukan kungiyar tare da bata hadin kai a duk lokacin da ake bukata.
You must be logged in to post a comment Login