Labarai
Al’umma su tallafawa ‘yaran da iyayen su suka rasu-HOLPI
Kungiyar tallafawa Marayu da marasa karfi wato Hope for Orphans and Less Privileged (HOLPI) ta jaddada kudirin ta na ci gaba da tallafawa talakawa masu bukatar tallafi a duk inda suke a nan Kano da ma kasa baki daya.
Adon hake ne kungiyar a ranar Larabar data gaba ta kai ziyara zuwa gidan marayu dake unguwar Nasarawa wato Children’s Home da wanda ke tudin maliki, Torrey Home a nan jihar Kano.
Kungiyar ta (HOLPI) ta ziyarci gidajen yaran ne domin duba irin halin da suke ciki tare da mika musu tallafin kayan amfanin yau da kullun.
Da take jawabi yayin ziyarar da kungiyar ta kai gidajen yaran shugabar kungiyar ta (HOLPI), Hajiya Bilkisu Sani Yola, cewa ta yi kungiyar ta (HOLPI) ta ziyarci gidajen ne don ganawa da yaran tare da sanya musu farin ciki a zuciyoyin su ta yadda za suji cewa dai-dai suka da ‘yayan dake zaune a gaban iyayen su.
Haka kuma yayin ziyarar kungiyar ta (HOLPI) ta rabawa ‘yaran kayan amfanin yau da kullim dana ciye-ciye don sanya farin ciki a zukatan su.
Hajiya Bilkisu Sani Yola ta kuma yaba bisa yadda shugabannnin gidajen yaran biyu suke kula da yaran yadda ya kamata wajen tsaftar kayan su, da wajen zamansu da abincin da suke ci.
Shugabar ta kuma yi kira ga al’ummar dake fadin jihar Kano dama kasar nan da su rinka taimakawa yaran dake zaune a gidajen don sanya walwala a zukatan su musamman donjin cewa suma dai-dai suke da kowanne yaro dake gaban iyayan sa.
Da take jawabi yayin ziyarar da kungiyar ta (HOLPI) ta kai, shugabar gidan marayu dake Nasarawa wato Nasarawa Children Home Hajiya Aishatu Sani Kurawa, godewa kungiyar ta yi bisa ziyarar da suka kai gidan don tallafawa yaran dake ciki musamman a wannan wata da muke ciki na A zumin Ramadan.
Itama a na ta jawabin shugabar gidan yara dake Tudin Maliki wato Torry Homme Hajiya Laure itama godewa kungiyar ta (HOLPI) ta yi bisa ziyarar da suka kai gidan don bayar da tallafi ga yaran dake zaune a ciki.
Covid-19: Mawadata su tallafawa wadan da basu dashi- HOLPI
Gabaki dayan shugabannin gidajen bisu sunyi kira ga sauran al’umma da su rinka tallafawa yaran dake cikin irin wadancan gidaje, a cewar su gwamnati kadai bazata iya daukan dawainiyar ub a, adon haka dole ne sai al’umma sun tallafa.
Ziyarar kungiyar ta (HOLPI) zuwa gidajen yaran dake Unguwar Nasarawa wato Children Home da wacce ke Tudin Maliki wato Tudin Maliki Torrey Home na kunshe ne ta cikin sanarwar da jami’in hurda da jama’a na kungiyar Ibrahim Abdullahi ya raba ga manema labarai a ranar Juma’ar data gaba 15 ga watan Mayu shekarar 2020
You must be logged in to post a comment Login