Manyan Labarai
Al’ummar Dakata sun koka akan ginin shaguna bisa magudanar ruwa
Al’ummar Dakata mazauna layin Sarauniya sun koka bisa abinda suka kira rashin adalcin da akayi musu, na yanka fili tare da aza harsashin ginin shaguna akan magudar ruwa .
Mazauna yankin sun tabbatar dacewa karamar hukumar Nassarawa ke da alhakin aikata haka kasancewar shaidun gani da ido sun tabbatar da hakan.
Al’ummar wanda suka nuna fushin su ta hanyar cincirindo a wajen da aka aza harsashin ginin , a safiyar yau sun tabbatarwa da Freedom Radio, cewar a baya shugaban karamar hukumar Nassarawa Alhaji Lamin Sani, ne da kansa ya jagoranci tawagar da ta duba wajen wanda a lokacin sun tsammanin cewar za’a yi aikin fitar da magudanar ruwa ne.
Amma sai gashi sun wayi gari da yanka wajen don samar da shaguna wanda hakan zai haifar musu da matsalar muhalli ga mazauna yankin.
Labarai masu alaka.
Lagos:mutane 18 sun rasa rayukansu sakamakon rushewar gini
Gwamnatin tarayya ta ware sama da naira biliyan biyu domin aikin dagwalon masana’antu a Kano
Mazauna layin , da aikin ya kusanci gidajen su , sun nuna bacin ransu dangane da yadda ake shirin gudanar da aikin, tare da yin kira ga hukumomin da lamarin ya shafa musamman ma na muhalli da kasa dasu shigo cikin lamarin tare da daukar matakan dakatar da aikin.
Sai dai duk da kokarin da mukayi na jin ta bakin shugaban karamar hukumar Nassarawa Alhaji Lamin Sani, hakan bai samu ba sakamakon bai amsa kiran waya ba, kuma bai turo amsar sakon kar ta kwana da muka aika masa ba.
Haka shima Kansilan yankin na Dakata, Umar Alasan Otu, ya ki cewa uffan dangane da yadda aikin yake da kuma waye yake da alhakin gudanar dashi.
Al’ummar sun yi kira ga gwamnatin jihar Kano, data yiwa tufkar hanci tare da dakatar da aikin kasan cewar ginin ba zai haifar da, da mai ido ga mazauna yankin ba.
A baya ma an samu korafe korafe da dama, makamantan wannan da ake zargin wasu daga cikin mukarraban gwamnati mai ci yanzu da yanka filaye na unguwanni, makabartu, kasuwanni da masallatai dake fadin jihar Kano tare da siyar dasu wajen yi gine –gine ba bisa ka’ida ba dake haddasa matsaloli ga al’umma, wanda hakan ya sa har wani babban jami’in gwamnatin hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa EFCC, ta kama tare da bincika bisa dalilai masu alaka da haka.
You must be logged in to post a comment Login