Connect with us

Labarai

Al’ummar Marghi sun nemi a ceto Ɗalibai 78 da Malami da aka yi garkuwa da su Borno

Published

on

Al’ummar Marghi a jihar Borno sun yi kira ga gwamnatin tarayya da gwamnan jihar, Babagana Zulum, da su ƙara ƙaimi wajen ceto ɗalibai 78 da wani malami da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Askira/Uba.

 

Al’ummar sun yi wannan kiran ne yayin wani taron manema labarai a Abuja, inda suka ce waɗanda aka sace sun shafe kwanaki 140 a hannun masu garkuwa da mutane.

 

A ranar 16 ga Mayu ne dai aka sace ɗalibai 42 daga makarantar Mussa, yayin da a ranar 29 ga Yuni aka yi awon gaba da ɗalibai 36 da wani malami daga makarantar sakandaren gwamnati da ke Lassa.

 

Sakataren al’ummar Marghi, Malla Gadzama, ya ce sace yaran a lokacin da suke neman ilimi ya jefa iyalansu cikin damuwa da rashin tabbas.

 

Ya roƙi shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu da ya umarci hukumomin tsaro da na leƙen asiri su ƙara ƙoƙari wajen tabbatar da sakin waɗanda aka sace.

Haka kuma, ya buƙaci Gwamna Zulum da ya sanya batun ceto daliban cikin abubuwan da yake tattaunawa da gwamnatin tarayya da hukumomin tsaro.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!